16 Satumba 2020 - 15:29
Iran Za Ta Mayar Da Martanin Da Ya Dace Ga Kowane Irin Kuskure Na Amurka

Kakakin gwamnatin Iran, Ali Rabie, ya bayyana haka ne da yake mayar da martani akan tsokacin shugaban kasar Amurka Donald Trump a Twitter akan cewa Iran tana son kashe jami’in diplomasiyyarta.

ABNA24 : Rabie ya kara da cewa; Abinda shugaban na kasar Amurka ya fada bai da tushe shaci fadai ne kawai.

Rabie ya kuma ce: “Muna takaicin ganin yadda shugaban kasar Amurka yake yin Magana akan gurbataccen rahoto, irin wacce ta kai ga shelanta yaki akan Iraki da Afghanistan a baya.”

Kakakin gwamnatin ta Iran ya ce; Gwamnatin Amurka, musamman ta wannan shugaban, tana son hargitsa zaman lafiya a cikin wannan yankin.

342/